Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta a ranar Alhamis ta soke nasarar Da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya samu.
A sakamakon haka, kotun ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.
Kotun dai ta ce za a sake zaɓen ne a wasu ƙananan hukumomin Jihar guda uku.
Ƙananan Hukumomin su ne Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukyun.
A cewar kotun, hukuncin da Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Gwamnan ya yi a baya, wanda ya tabbatar da nasarar Dauda, bai yi la’akari da hujjar da jam’iyyar APC mai ƙara ta gabatar ba.
KU KUMA KARANTA: Gwamna Lawan ya amince da naira biliyan huɗu don gyara hanyoyi a Gusau
Kazalika, kotun ta yi fatali da sakamakon da APC da kuma Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta bayar a ƙaramar Hukumar Maradun.
Tsohon Gwamnan Jihar, kuma ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle ne dai ya shigar da ƙarar yana neman a soke nasarar Dauda a zaɓen.
Hukumar INEC dai ta bayyana Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.