Kotu ta da ɗage sauraron ƙarar Abdullahi Ganduje kan zargin badaƙalar kuɗaɗe
Daga Jamilu Lawan Yakasai.
Wata babbar kotun jihar Kano ta ɗage ci gaba da zamanta har zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, inda za ta ci gaba da sauraren ƙara bisa zargin cin hanci da rashawa akan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje da wasu mutane bakwai.
Gwamnatin jihar ta shigar da ƙara kan tuhume-tuhume takwas da suka hada da zargin karbar rashawa, almundahana da kuma raba kudaden jama’a da suka kai biliyoyin Naira akan Ganduje, tare da matarsa, Hafsat Umar.
Sauran sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited da Lasage General Enterprises Limited.
Lauyan Ganduje da matarsa da Umar, Lydia Oluwakemi-Oyewo, sun shaida wa kotun cewa a shirye ɓangaren su yake a ci gaba da shari’ar..
Lauyan wanda ake kara na 3 da na 7, Adekunle Taiye-Falola, ya shaida wa kotun cewa bai shirya gabatar da karar sa na farko ba.
KU KUMA KARANTA:Kotu ta sa ranar gurfanar da Ganduje da matarsa Hafsat
Alkaliyar kotun, Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta amince da duk takardun neman karin lokaci.
Misis Adamu-Aliyu ta dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 15 ga Afrilu, 2025 domin sauraron duk wasu korafe-korafe da ake
A lokacin da shari’ar ta zo domin sauraren duk wasu kararraki da ake yi, a ranar Alhamis, Lauyan jihar, Adeola Adedipe, SAN, ya shaida wa kotun cewa a shirye yake a ci gaba da shari’ar.
Adedipe ya shigar da karar ne a kan sanarwar da aka shigar a ranar 5 ga watan Fabrairu, inda ya nemi a kara musu lokaci domin su daidaita takaddamarsu ta farko da masu amsa na 1, 2 da 4 suka shigar.