Kotu ta ƙi amincewa a saki bayanan kadarorin Buhari da Jonathan

0
148

Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar buƙatar sako bayanan kadarorin tsofaffin shugabannin Najeriya, da suka haɗa da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari da mataimakansu Namadi Sambo da Yemi Osinbajo.

Wasu ƙungiyoyi biyu ne suka rubutawa hukumar ɗa’ar jami’an gwamnati CCB ta fito da bayanan bisa dokar ‘yancin samun bayanai ta 2011.

Ƙin fidda bayanan ya sa ƙungiyoyin shigar da ƙarar buƙatar tilastawa hukumar ta saki bayanan.

KU KUMA KARANTA:An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi wajen cire dala 6.2m daga CBN — Boss Mustapha

Bayan rashin nasara a babbar kotun tarayya, ɗaya daga ƙungiyoyin ta ɗaukaka ƙara, amma nan ma kotun ta ce ba zai yiwu a saki bayanan ba, ba tare da tsari daga majalisar dokoki ba kamar yadda yake a tsarin mulki.

Kotun ta ce da ƙarar Majalisa ya dace a shigar don tilasta ta sako tsarin don samun hurumin fidda bayanan.

Mai ɗaukaka ƙarar Chido Onuma ya ƙi amincewa da hukuncin yana mai alwashin garzayawa kotun ƙoli.

Onuma ya zargi sashen shari’a da kawo tarnaki a samun bayanai daga gwamnati.

Leave a Reply