Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Kotu a Anambara ta yanke wa tsohon ma’aikacin banki hukuncin ɗaurin shekara 121

Wata kotu a Jihar Anambra da ke Kudancin Najeriya ta yanke wa wani tsohon ma’aikacin banki hukuncin ɗaurin shekara 121 a gidan yari.

Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Najeriya Zagon-Ƙasa wato EFCC ce ta shigar da shi ƙara inda ta zarge shi da almundahana ta naira miliyan 112.

Mai Shari’a S.N. Odili ne ya yanke wannan hukuncin bayan ya samu Nwachukwu Placidus wanda tsohon manaja ne a bankin FCMB da laifin almundahana ta naira miliyan 112,100,000.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an gurfanar da shi ne a ranar Talata 27 ga watan Maris ɗin 2018 kan zarge-zarge 16 waɗanda suka haɗa da laifin yin jabu da sata da ƙarya.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Sai dai Mista Placidus ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa bayan an karanto masa su a kotu.

“A lokacin shari’ar, EFCC ta hanyar lauyanta Mainforce Adaka Ekwu ya gabatar da shaidu huɗu waɗanda suka bayar da takardu masu muhimmanci a matsayin hujjoji,” in ji sanarwar.

Mai shari’a Odili ya yanke wa Mista Placidus hukuncin ɗauri na shekara tara bisa zargi na biyu sai hukuncin ɗaurin shekara huɗu kan zargi na huɗu.

Sannan Mai Shari’ar ya yanke masa hukuncin ɗauri na shekara tara-tara kan zargi na biyar har zuwa na zargi na 16.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *