Connect with us

Harkokin Mata

Ko ka san amfanin jigida a jikin mace?

Published

on

Jigida wani abu ne da ake sanyawa a ƙugu wadda mata ke amfani da shi, kamar sauran ababen kwalliyar gargajiya irin su; Agogo, Awarwaro, Sarƙar Wuya, Zobe, da ‘yan kunne da mata ke sanyawa a jikinsu. Kwalliyar ƙugu dai, mata ne ke yi domin kwalliya.

A zamanin baya, matan nahiyar Afirka suna sanya Jigida ne a matsayin alamar mace da kuma jan hankali.

Wasu kuma sun yi imanin sanya Jigida na taimaka musu wajen lura da nauyinsu.

KU KUMA KARANTA: Mace ɗaya ‘tilo’ mai gyaran wayar salula a jihar Borno

A wasu yankunan ana haɗa jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen ɓoye, wato aljanu.

Wani jigidan akan haɗa da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman ƙananan yara.

Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun sauƙin naƙuda a lokaci haihuwa.

Akwai yaƙinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage ƙiba musamman ga mata masu tumbi ko ƙaton ciki.

Jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman ƙugu wato ‘Hips’ a Turance, da kuma samun farin jini cikin mutane.

Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Taliban ta haramta wa matan Afganistan yin kayan kwalliya, da rufe waɗanda ake da su | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Harkokin Mata

Ko me ke janyo shanyewar ƙafa ga uwa bayan haihuwa?

Published

on

Daga cikin matsalolin da iyaye mata ke fuskanta yayin naƙuda wadda ke hana su tafiya bayan haihuwa saboda raunin ƙafafu akwai matsalar nan da ake cewa “Maternal Obstetric Palsy” a turancin likita.

Wannan matsala na faruwa ne yayin naƙuda a lokacin da kan jariri ya sauƙo zuwa ƙugun uwa. Tsawaitar naƙuda ko kuma tangarɗar naƙudar kan sa kan jariri ya danne gungun jijiyoyin laka da suka sauƙo zuwa ƙugu da ƙafafu da ake cewa “lumbosacral plexus” a yaren likita.

Duk da cewa wannan matsala tana iya shafar ƙafafu biyu a lokaci guda, amma ta fi shafar ƙafa ɗaya.

Iyaye mata da suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1] Gajeru; saboda ƙuncin ƙugu.

2] Naƙuda da haihuwar jaririn da kansa ya wuce matsakaicin girma, wato girman kan jaririn ya fi faɗin mafitar ƙugun.

3] Nawa ko tsawaitar naƙuda fiye da yadda aka saba gani.

4] Uwayen da suka gaza haihuwa da kansu har sai da aka temaka musu da maƙatar ungozoma domin zaƙulo kan jaririn, wato “forcep delivery” a turance.

5] Juyewa ko karkacewar jariri yayin naƙuda da sauransu.

Alamun larurar sun haɗa da:

Waɗansu alamun suna bayyana tun a lokacin naƙuda, a yayin da wasu kuma kan bayyana bayan haihuwa.

KU KUMA KARANTA: Dalilan da ya sa maganin tazarar haihuwa ke haifar da illoli ga mata

1] Ciwo daga cinya zuwa tafin sawu.

2] Rashin jin daɗi a fatar ƙafar; kamar jin tafiyar kiyashi, jin dindiris, jin kamar ana tsira allura, ko kuma jin kamar jan wutar lantarki. 

3] Shanyewar ko raunin ƙafafu da tafin sawu.

4] Ƙwacewar fitsari da da ko bahaya.

5] Matsalar saduwa da iyali, da dai sauransu.

Sai dai, sau da yawa a kan bar iyaye matan da suka haihu a kwance saboda sun kasa tashi sakamakon rashin ƙwarin ƙafafunsu ba tare da an ɗauki matakan da suka kamata ba.
 
A yayin da mace ta haihu, sannan aka lura ta kasa taka ƙafafunta a tuntuɓi likitan fisiyo domin ɗaukar matakan da suka kamata.

Continue Reading

Harkokin Mata

Dalilan da ya sa maganin tazarar haihuwa ke haifar da illoli ga mata

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

A wannan rubutu da Aisha Salisu Babangida ta yi, a kan wannan matsala ta fara ne da cewa; Magungunan hana ɗaukar ciki sun zama muhimmin al’amari ga ma’aurata, musamman ma mata da ke amfani da su wajen ba da tazarar haihuwa da tsara rayuwar iyali.

Irin waɗannan magunguna, sun ƙunshi hanyoyi daban-daban, kama daga magungunan sha zuwa allurai da robar da ake sanya wa mata a dantsensu, da dai sauransu.

Da yawan mata na ganin fa’idar amfani da magungunan hana ɗaukar ciki, amma wasu sun ce sukan fuskanci matsaloli da dama da ke zuwa bayan amfani da su.

Waɗansu matsalolin da mata ke fuskanta sakamakon amfani da magungunan hana ɗaukar ciki kamar yadda Maryam da Faiza, wasu iyaye mata masu amfani da irin waɗannan magunguna suka shaida wa BBC, su ne; matsalolin al’ada da ƙarin ƙiba da amai.

KU KUMA KARANTA: Abincin Najeriya da masu neman haihuwa ya kamata su ci

Akwai ma ciwon Nono da ciwon kai da rage sha’awar jima’i da fitowar wani ruwa daga al’aura da dai sauransu.

Waɗannan matsaloli suna kuma haifar da rashin jituwa a tsakanin ma’aurata in ji su.

Continue Reading

Harkokin Mata

Afganistan ta ba da damar ɗalibai mata su halarci jami’o’i a ƙasar – Hukuma

Published

on

Wani kwamiti na ma’aikatar ilimi mai zurfi ta Afganistan ta ce yana kan shirin sake buɗe jami’o’i ga ɗalibai mata, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito a ranar Litinin.

Kwamitin ya bayyana hakan ne a lokacin wani rahoto na shekara-shekara na ma’aikatar.

“Za mu raba shi da jama’a idan an kammala shirin,” in ji rahoton.

KU KUMA KARANTA: Taliban ta haramta wa matan Afganistan yin kayan kwalliya, da rufe waɗanda ake da su

Muƙaddashin ministan ilimi mai zurfi Lutfullah Khairkhwa ya ce har yanzu ba a bayyana lokacin kammala shirin ba.

Ya zuwa yanzu dai an hana mata shiga jami’o’i a ƙasar Afganistan.

Ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta sanar da hana ilimin mata a watan Disamba 2022.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like