Ko a mafarki jam’iyar APC ba za ta iya lashe zaɓe a Kano ba – Shugaban jam’iyar NNPP na Osun

0
6
Ko a mafarki jam'iyar APC ba za ta iya lashe zaɓe a Kano ba - Shugaban jam'iyar NNPP na Osun

Ko a mafarki jam’iyar APC ba za ta iya lashe zaɓe a Kano ba – Shugaban jam’iyar NNPP na Osun

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya caccaki Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, kan shirin jam’iyyarsa na karbe mulki a Kano a zaben gwamna na gaba.

Da ya ke kwatanta wannan shiri da mafarki mara tabbas, Odeyemi ya ce hakan ya nuna yadda Ganduje ya yanke hulda da talakawa, wadanda ya ce suna goyan bayan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf.

KU KUMA KARANTA:Na gaji bashin Naira biliyan 8.9 a asusun APC bayan zama na shugaban jam’iyyar – Ganduje

Da ya ke mayar da martani kan wata sanarwa da aka danganta da Shugaban APC na kasa, wanda ya siffanta NNPP a matsayin jam’iyya da ke gab da mutuwa a Kano, Odeyemi a cikin wata sanarwa ya ce wajibi ne Ganduje ya farka daga wannan mafarkin na gangan na karbe jihar.

Sanarwar ta ce:“Gaskiyar halin da ake ciki a Kano a yau ya wuce abin da tsohon gwamna zai iya raina wa haka kawai.

“Na yi dariya lokacin da na ga wannan magana. Ko da yake shekaru sun ja wa Baba Ganduje, ba zan zarge shi sosai ba, amma dai ina so ya fahimci cewa Kano ta canza.

“In ba haka ba, ta yaya wani da ke zaune nesa da jiharsa zai rika shelar cewa manyan NNPP suna shirin ficewa daga jam’iyyar mai mulki a Kano zuwa APC, kawai saboda ya jagoranci rabon motocin hawa guda 63 da babura guda 1,137 ga shugabannin APC na kananan hukumomi da mazabu a jihar?

“Talakawan Kano suna tare da Gwamna Abba Yusuf, wanda ke kokarin yin duk mai yiwuwa don kyautata rayuwarsu ta kowane bangare.

Leave a Reply