KNUPDA ta rushe gine-ginen da akayi ba bisa ƙa’ida ba a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Ana zargin rumfar shagon wata matashiyar ‘yar tiktok wato Rahama Sa’idu aikin ya rutsa da ita.
A safiyar Alhamis din nan matashiyar ta garzaya Hukumar Karbar Korafi ta Kano karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, inda ta zargi an cire mata allon sanarwa ba tare da an sanar mata ba, sai dai hukumar tace anbi ka’ida gabanin daukar hukuncin.
Wadda ta saki wani bidiyo a kafar sadarwa, take nuna cewar Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ne yabada umarnin cire mata, hartakai mabiya Gwamnatin Kano sun fito sun fara yi mata martani, sakamakon rashin tarbiyya da suke zargin rayiwa Jagoran gwamnatin su. Wanda suka ce Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da Hana cin hanci da rashawa ta Kano, Barr Muhuyi Magaji Rimi Gado, ya ci mutuncin babban jami’in Gwamnati na ma’aikatar Knupda.
KU KUMA KARANTA:Ministan tsaron Saudiyya ya gana da shugaban addini na Iran Khamenei, ya miƙa masa wasiƙar Sarki Salman
Wanda suka ce ya yi mishi tsawa a cikin wani fefen bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta.
A yammacin wannan rana kuma hukumar ta KNUPDA ta kammala aikin rushe ragowar gurin da suka ce matashiyar ‘yar tiktok din tayi cin hanya.









