KMT ya ba da tallafin Naira miliyan 1 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Gulani
Alhaji Kashim Musa Tumsa MFR (KMT) ya ba da tallafin Naira miliyan ɗaya (one million) ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a ƙauyukan Bara, Biyi, Duchi, shishiwaji da Ndubulwa da ke ƙaramar hukumar Gulani a jihar Yobe.
Daraktan harkokin mata ta KMT-BOND 2027, Hajiya Fatima Ahmed Godowoli ce ta jagoranci tawagar ba da tallafin.

KU KUMA KARANTA: An ƙaddamar da buɗe gadar da KMT ya gina a Rugar Fulani Potiskum (Hotuna)
Dagacin yankin, ya yi jawabin godiya ga Kashim Musa Tumsa akan wannan tallafi da ya musu. A madadin dukkan al’ummar yankin, ya miƙa godiya ga KMT tare da fatan alheri da addu’ar Allah ya biya masa dukkan buƙatunsa, ya cika masa burinsa da ya saka a gaba.










