Kiristoci sun taya musulmi gyaran masallacin Idi a Kachia

0
172

Daga Maryam Sulaiman

A ranar Asabar da ta gabata ne, dandazon Kiristoci suka taya musulmi gyaran babban masallacin Idi a garin Kachia dake jihar Kaduna. Kiristocin sun fito ne maza da mata domin taya al’ummar musulmi sare ciyawar dake Masallacin Idin, kamar yadda suka yi a shekarar da ta gabata.

Mercy Bajimi, tana ɗaya daga cikin Kiristocin da suka fito taya musulmin sare ciyawar dake filin masallacin Idin, ta shaida wa manema labarai cewa “mun zo ne mu taya ‘yan’uwanmu musulmi domin a gyara wurin da za a yi Sallar Idi, a yi addu’a, a yi Ibada cikin walwala da kwanciyar hankali”.

“Muna cikin aikin gyaran filin Idin, sai ga tawagar Kiristoci sun iso, suna da yawa, maza da mata, suka shigo muke aikin tare da su, kamar yadda suka yi a shekarar da ta gabata” inji wani Musulmi.

KU KUMA KARANTA: Labari cikin hotuna: Yadda Kiristoci suka taya Musulmi gyaran filin Sallar Idi

“Muna yin abubuwa da yawa waɗanda suke ƙara mana zaman lafiya da ƙaunar juna. Muna ziyartar juna idan abin farin ciki ya faru ko na baƙin ciki. Sannan muna shirya cin abincin Sallah a lokutan bukukuwan Sallah da na Kirsimeti” inji Malam Ibrahim Tasiu

Jagororin addini a yankin sun yi fatan irin wannan zumunci ya ɗore har abada.

Leave a Reply