Daga Haruna YUSUF, Abuja
Sanata Orji Uzor Kalu ya koka da yadda ake ci gaba da fama da ƙarancin takardun naira a Najeriya sakamakon matakan da babban bankin Najeriya (CBN) ya ɗauka na sake fasalin kuɗin ƙasar.
Sanata mai wakiltar mazaɓar Abia ta arewa a lokacin da yake mayar da martani game da matsalar kuɗi da ake fama a halin yanzu, ya ce iyalansa ba za su iya samun isassun kuɗin da za su yi girki ba.
Sanatan wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne, ya bayyana haka ne a ranar litinin a lokacin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels, wanda jaridar Neptune Prime ta bibiya.
“Kuna iya ganin manufar ya yi ƙaranci yayi daidai? Amma Ni ba na ajiye kuɗi a gidana, Ina shan wahala,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: CBN zai hukunta duk bankunan da ke ɓoye sabbin kuɗi
“A kwanakin baya, manajan gidana ya gaya wa matata da ke Abuja cewa ba mu da kuɗin da za mu dafa abinci.
“Matata kusan tana yawo kuma muna ciyar da mutane sama da 250 kowace rana. Wannan matsala ce a gare ni da kuma ga kowa da kowa.”
Jigon na jam’iyyar APC ya kasance na baya-bayan nan a cikin jiga-jigan jam’iyyar da suka fito fili suka yi magana kan ƙarancin naira tun bayan da babban bankin ya dage kan wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.
Idan dai ba a manta ba kotun ƙoli ta bayar da umarnin cewa tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000 na nan daram, biyo bayan umarnin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a makon da ya gabata a ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu a jawabinsa na ƙasa ya tsawaita amfani da tsohuwar takardar naira 200 kawai, har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.
Sai dai kuma hakan bai yi wa wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki daɗi ba, waɗanda ke da ra’ayin cewa sai an yi amfani da tsohuwar takardar naira a jihohinsu.
Da yake la’akari da lamarin, Sanata Kalu ya bayyana ra’ayi ɗaya da gwamnonin, inda ya ce da ya yi biyayya ga umarnin kotun ƙoli kan kuɗin naira idan shi ne shugaban ƙasa.
Ya ce, “Don haka ne idan na kasance a matsayin shugaban ƙasa kamar yadda na faɗa muku a baya, zan saurari hukuncin kotun koli.
“Kotun ƙoli a gare ni, ko suna da gaskiya ko ba daidai ba, ya kamata shugaban ƙasa ya bi doka kuma ya nemi babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami, da ya sake duba kotun ƙoli.”
Sanata Orji Kalu ya ba da tabbacin cewa APC za ta yi nasara a zaɓukan duk da rashin samun kuɗin da ake da wasu gwamnonin ciki har da Sanatoci suka yi ikirarin hakan zai shafi kayan aiki a lokacin zaɓe.