Kasafin kuɗin 2023: Gwamna Sule zai fara aiki gadan-gadan

0
500

Gwamnan jihar Nasarawa injiniya Abdullahi Sule ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2023 da ya kai sama da naira biliyan 149.3 inda ya ce gwamnati za ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba wajen aiwatar da kasafin gaba ɗaya, domin amfanin jihar baki daya.

Kasafin kuɗin, wanda aka yiwa laƙabi da budget of consolidation and continuity, ya an miƙa shi gidan gwamnati Lafia inda gwamnan ya yaba wa kakakin majalisar jihar Ibrahim Balarabe Abdullahi, da ɗaukacin ‘yan Majalisu bisa gaggauta amincewa da takardar bisa kishin da suke da shi ga Jihar.

An gabatar da kasafin kuɗin a zauren majalisar dokokin jihar a ranar 22 ga Nuwamban 2022 kuma ‘yan majalisar suka amince da shi a ranar 20 ga Disamban 2022, gwamna Abdullahi Sule ya bayyana kasafin kuɗi na Naira biliyan 149.3.

KU KUMA KARANTA:Ba zan yi amfani da kuɗin talakawa wajen neman tazarce ba – Abdullahi Sule

Gwamna Sule wanda ya cika da tsare-tsaren da suka kai ga rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗi na ashirin da uku a matsayin doka, ya ci gaba da cewa kasafin kuɗin da aka yi wa lakabi da kasafin bunkasa tattalin arzikin ƙasa da ci gaba, zai baiwa gwamnati damar gudanar da ayyukan da ba su da alaka da gwamnati, samar da shirye-shirye masu dacewa da mutane.

A cewar Gwamnan, tare da ƙudurin tabbatar da ci gaba da tsare-tsare da na gwamnati, ayyukan siyasa da ke gudana ba za su shafi aiwatar da shirye-shiryen gwamnati ba.

Tun da farko kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi ya bayyana cewa, ‘yan majalisar sun tabbatar da cewa ƙudurin kasafin kuɗin ya bi tsarin doka, kafin daga bisani a zartar da shi, don haka ya yaba wa shugabannin ma’aikatun gwamnati da na ƙananan hukumomi da kuma kwamitin kuɗi na majalisar bisa jajircewarsu har zuwa yanzu.

Shugaban majalisar ya kuma yi fatan samun ɗorewar haɗin gwiwa tsakanin ‘yan majalisa da ɓangaren zartaswa na gwamnati a cikin lokaci mai zuwa domin samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar.

Leave a Reply