Kamfanoni a Najeriya na fuskantar barazanar durƙushewa
Ƙungiyar Kamfanoni a Najeriya (MAN) ta bayyana cewa, tana fuskantar barazanar durƙushewa, kasancewar a yanzu haka, kayayyakin da suke sarrafawa a ƙasar na zamo musu kwantai sakamakon tsadar kayan sarrafawa.
Kungiyar ta koka bisa yadda kudin gudanarwar kamfanonin kasar ya karu da kaso 357.57, sai kuma koma-baya na kaso 1.66 a cinikin kayan da suke sarrafawa.
Kungiyar ta ce yanzu kayayyakin da suke sarrafawa na zamo musu kwantai, saboda babu masaya, ganin cewa irin karin farashi da suka yi wanda ya zamo tilas, saboda karin farashin makamashin wutar lantarki da kaso 200 da gwamnatin tarayya ta yi, sai kuma karanci da kuma tsadar canjin dalar Amurka, hadi da karin kudin ruwa da babban Bankin Najeriya yayi.
KU KUMA KARANTA:Takardar Naira 100 ta fara ƙaranci a cikin al’umma
MAN, ta ce, a rubu’in farkon shekarar 2024 ta fuskanci kwantan kayayyakin da suka sarrafa da ya haura Naira Triliyan 1.24.
Kazalika, kungiyar ta masu masana’antu ta yi kira yi ga gwamnatin kasar da ta duba lamarin, domin ta haka ne masana’antun zasu iya tsayawa da kafafun su.
A hirarsa da Muryar Amurka Farfesa Hussaini Usman Malami, Masani kuma malami a tsangayar tattalin arziki dake jami’ar Usman Danfodiyo a jihar Sokoto, ya ce dole masana’antu a kasar su shiga irin wannan mayuwacin hali, saboda yanzu tsadar rayuwa ta sa mutane a kasar basa sayen kayayyakin da bai zamo musu tilas ba, Bisa ga cewarsa, karin kudin haraji da gwamnatin kasar ke yi, na mayar da hannun agogo baya, domin masana’antun suna ji a jika.
A nashi bayanin, Hassan Sardauna, daya daga cikin masu sharhi kan lamuran yau da kullum, na ganin wannan barazana da kamfanonin kasar ke fuskanta abu ne da yakamata a dauki mataki tun wuri.
Masana dai na ganin sabbin tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta zo dashi, ɗanyen itace ne mai wahalar lanƙwasa.