Kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur

0
88
Kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur

Kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya sake ƙara farashin litar man fetur, Naira 1,020 a Jihar Legas, yayin da a Babban Birnin Tarayya, Abuja ake sayar da litar kan Naira 1,050.

Wannan sabon ƙarin na zuwa ne mako uku da ƙarin da kamfanin NNPCL ya yi.

A ranar 9 ga watan Oktoba 2024 ne kamfanin ya kara farashin litar zuwa Naira 1,030 a Abuja, sai kuma farashin ya tashi a Jihar Legas daga 897 zuwa Naira 998.

Rahotann daga gidajen man NNPC sun tabbatar da cewa a Legas farashin yana kai wa har 1,025 kan kowace lita.

Ƙarin farashin na zuwa yayin da ‘yan Najeriya suka fara rage amfani da mai saboda tsadar da ya yi tare da samun raguwar ababen hawa a kan tituna.

KU KUMA KARANTA: Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu; Rahoto

Wasu alƙaluma sun nuna cewar ‘yan Najeriya sun rage amfani da litar, wanda daga lita miliyan 60 a kowace rana ya dawo zuwa lita miliyan 4.5 a watan Agustan 2024.

Leave a Reply