Jirgin sama na Emirates ya dawo da jigila a Najeriya

0
49
Jirgin sama na Emirates ya dawo da jigila a Najeriya

Jirgin sama na Emirates ya dawo da jigila a Najeriya

Kamfanin Jiragen Sama na Emirate mallakin Hadaddiyar Daular Larabawa ya sauƙa a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Talata, bayan kusan shekaru biyu da ya dakatar da ayyukansa saboda tangarɗar diplomasiyya da kasa kwashe kuɗaɗensa daga ƙasar.

Jirgin mai lamba EK 783 ya sauƙa a filin jiragen sama na MMIA da misalin karfe 3:32 na ranar Talata, inda rahotanni suka ce babu mutane da yawa a cikin jirgin samfurin Boeing 777.

Ba a gudanar da wani bikin sauƙar jirgin ba da tankar ruwa ko shewa, sakamakon samun labarin gudanar da zanga-zanga a Najeriya da kamfanin ya samu.

Jirgin zai dinga jigilar fasinjoji a kowace rana tsakanin Dubai da Legas.

A makon da ya gabata Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun amince kan yarjejeniyar sauƙe hakkokin juna, inda Emirate zai dinga zuwa Najeriya, haka shi ma jirgin kamfanin Air Peace zai dinga zuwa Dubai yana dawo wa Legas.

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Festus Keyamo, tare da mahukuntan sufurin jiragen sama na HDL sun amince kan sabuwar yarjejeniyar Huldar Jiragen Sama (BASA) tsakanin ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA: Kamfanin Emirates ya yi sulhu da gwamnatin Najeriya, zai ci gaba da tashi daga Legas

An rawaito ministan na cewa “Tattaunawar mai muhimmanci ta samar da yarjejeniyar sauke hakkokin juna, tare da tabbatar da cewa jiragen saman Najeriya ma za su samu damar fara tashi kai tsaye zuwa HDL.

Wannan cigaba ne mai tarihin gaske ga sashe sufurin jiragen saman Najeriya, inda matafiya suka samu damar faɗaɗa zirga-zirga zuwa kasashen waje.”

A matsayin na babbar cibiyar kasuwanci a Afirka, Najeriya ta ƙulla kakkarfar alaƙar cuɗe ni in cuɗe ka da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tsawon shekaru.

Haka zalika baya ga jirgin fasinja, bangaren jigilar kaya na Emirates Skycargo ma zai taka rawa wajen habaka kasuwanci zuwa Najeriya da fita da kaya daga kasar zuwa waje.

Kamfanin ya ce zai tallafa wa kasuwancin Najeriya ta hanyar fitar da kayayyakin ƙasar zuwa Dubai, daga nan kuma zuwa ƙasashen Malaysia, Hong Kong, Bahrain da sauran su.

Kamfanin zai kuma dinga shigo da wasu kayyaki zuwa Najeriya daga manyan kasuwanin HDL, India da Hong Kong.

Leave a Reply