Aƙalla mutane huɗu ne suka mutu, wasu da dama suka samu raunuka bayan wani jirgin ƙasan fasinja ya yi hatsari a Jihar Bihar ta ƙasar Indiya.
Rahotanni sun ce jirgin ƙasan ɗauke da fasinjoji zuwa birnin Delhi daga tashar Anand Vihar, taragansa 21 ne suka sauƙa daga layin dogo a daren Laraba.
A safiyar Alhamis wani babban jami’in sufurin jiragen ƙasa, Tarun Prakash, ya sanar cewa “ana ci gaba da aikin ceto amma mutum huɗu sun mutu, wasu da dama sun jikkata bayan hatsarin jirgin ƙasan.”
Ministan sufurin jiragen ƙasa, Ashwini Vaishnaw ya jajanta wa waɗanda hatsarin ya shafa, yana mai cewa an sauya wa fasinjojin jirgi domin ƙarasa tafiyar tasu, amma mai yi magana kan mamatan ba.
Sai dai rahotanni sun ce an garazaya da waɗanda suka samu rauni asibiti domin ba su kulawa.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 24 a Peru, 21 sun samu raunuka
Indiya na daga ƙasashe da mafiya amfani da jiragen ƙasa, kuman an sha samun haɗura, mafi munin shi ne wanda mutum 800 suka rasu a shekarar 1981 sakamakon faɗuwar wani jirgin ƙasa a cikin kogi daga saman gadar jihar Bihar.
A watan Yuni mutum 300 sun mutu a sakamakon taho-mu-gaman jiragen ƙasa a Jihar Odisha sannan a Agusta wasu tara suka rasu a gobarar da ta tashi a taragon wani jirgin fasinja a yayin da fasinjoji ke haɗa shayi.