Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya

0
80

Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya

Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya a safiyar wannan Lahadin.

Jirgin wanda ya baro Kaduna ya kauce hanya ne da misalin karfe 9:30 na safiya a daidai yankin Jere da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce wannan lamari dai ya katse hanzarin gomman fasinjojin da jirgin ya ɗauko.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da ƙoƙarin gyara jirgin wanda kusan taragonsa guda uku suka sauka daga hanya.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar

Tuni dai jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da ’yan sanda suka isa wurin da jirgin ya yi hatsari da ke tsakanin wasu duwatsu.

Leave a Reply