Jirgin ƙasa ya tsallake rijiya da baya a hanyar Abuja zuwa Kaduna (Bidiyo)

4
377

Fasinjoji sun yi tattaki yayin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya tsallake rijiya da baya.

An tilastawa fasinjoji sauka tare da jigilar kayansu da ƙafa a lokacin da wani jirgin ƙasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ba zato ba tsammani ya kauce daga hanyar da ya nufa, ya bi ta wata hanya.

A cikin wani faifan bidiyo da aka ɗauka, wani mutum ya yi nuni da cewa lamarin zai iya yin muni da jirgin yana gudu.

Ya yi godiya, ya ce, “Allah ya kiyaye, ga layin namu da yakamata mu bi, sai mu ka bar hanyar”.

Kalli bidiyon a nan:

4 COMMENTS

Leave a Reply