Jihar Yobe ta cika shekaru 32 da zama jiha

1
250

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jihar Yobe tana ɗaya daga cikin jihohi guda Tara (9) da tsohon shugaban ƙasa Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ya ƙirƙiro a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1991. Jihohin sune; Abia, Enugu, Delta, Jigawa, Kebbi, Osun, Kogi, Taraba da Yobe. Ƙarin jihohi 9 da IBB ya yi a shekarar 1991, shi ne ya mayar da jihohin Nijeriya 30 cif-cif. A shekarar 1996, Janaral Sani Abacha ya ƙara jihohi guda Shida (6). Sune Ebonyi, Bayelsa, Nasarawa, Zamfara, Ekiti da Gombe. Shi ne ya mayar da jihohin Nijeriya 36.

Jihar Yobe tana da ƙananan hukumomi guda 17. Sune Damaturu, Potiskum, Bade, Machina, Jakusko, Fika, Fune, Nangere, Nguru, Gujba, Gulani, Yusufari, Yunusari, Tarmuwa, Gaidam, Bursari da Karasuwa.
A duk ranar 27 ga watan Agusta na kowace shekara ana tuna wa da wannan rana mai muhimmanci a Jihar Yobe.

Alhaji Sani Ahmad Daura shi ne gwamnan jihar Yobe na farko. Ya mulki jihar Yobe daga 1991 zuwa 1992. Ya sauka ne sakamakon zaɓe da aka yi a wannan shekarar. Alhaji Bukar Abba Ibrahim shi ne ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar SDP. Ya mulki jihar ne daga Janairun shekarar 1992 zuwa Nuwamban shekarar 1993. Ya sauka ne sakamakon rushe zaɓen da aka yi a duk faɗin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Yobe ta ɗauki ma’aikata 2,670 waɗanda suka kammala karatun digiri

Com-Pol Dabo Aliyu shi ne gwamnan jihar Yobe na uku, daga 1993 zuwa 1996. Wing Commander John Ben Kalio shi ne gwamnan jihar Yobe na Huɗu. Ya mulki jihar Yobe daga 1996 zuwa 1998.
Kanal Musa Muhammad shi ne gwamnan jihar Yobe na Biyar. Ya mulki jihar Yobe ne daga 1998 zuwa 1999. Yana kan mulki aka yi zaɓen Dimokraɗiyya na shekarar 1999. Alhaji Bukar Abba Ibrahim ne ya sake lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar APP. Inda aka sake zaɓensa a karo na biyu a ƙarƙashin jam’iyar ANPP. Ya yi shekaru 8 yana mulkin jihar Yobe.

An sake zaɓe a shekarar 2007, wanda marigayi Sanata Mamman B. Ali ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar ANPP. Sanata Mamman B. Ali shekaru biyu ya yi yana mulkin jihar Yobe, sai Allah ya masa rasuwa. Ya rasu yana kan kujerar gwamnan. Rasuwarsa ne yasa aka rantsar da mataimakinsa, Alhaji Ibrahim Gaidam a matsayin sabon gwamnan jihar Yobe.

Alhaji Ibrahim Gaidam, shekaru 10 ya yi yana mulkin jihar Yobe. Ya ƙarasa shekaru biyu na Marigayi Sanata Mamman B. Ali, sannan an sake zaɓen shi a karo biyu. Wato 2011 da 2015. Ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2019.
Alhaji Mai Mala Buni shi ne ya gaje shi. Daga 2019 zuwa 2023, kuma shi ne ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam’iyar APC a zaɓen 2023..
A shekaru 32 jihar Yobe ta yi gwamnoni 8 kenan.

A waɗannan shekaru 32, waɗanne nasarori aka samu, sannan a wane wuri aka gaza.
Idan za a duba yadda siyasa ta kasance a jihar Yobe tun dawowar Dimokraɗiyya a shekarar 1999, za a iya cewa an fafata sosai daga 1999 zuwa 2007. Amma daga shekarar 2007 siyasar adawa ta yi sanyi sosai a jihar Yobe. A Yobe ta Kudu (Zone B) ne kaɗai ake siyasa mai zafi har yanzu. Wadda ake fafata wa tsakanin jam’iyyu. Amma a sauran sassan jihar Yobe kam, jam’iya mai mulki ce take lashe kusan dukkan kujerun da ake zaɓen. In ban da zaɓen 2019 wanda ɗan majalisar jiha mai wakiltar Nguru I ya lashe zaɓen a ƙarƙashin jam’iyar PDP, shi ma daga baya ya koma jam’iyar APC mai mulkin jihar. Sai kuma a wannan babban zaɓe na 2023, shi ma dai jam’iyar PDP ita ce ta lashe kujerar Nguru II, wanda ya kayar da kakakin majalisar jihar Yobe.

Allah ya albarkaci jihar Yobe da al’ummar cikinta.

Ibraheem El-Tafseer Potiskum
eltafseerpen@gmail.com

1 COMMENT

Leave a Reply