Jihar Oyo za ta rushe dukkan shagunan da ke jikin katangar makarantu

0
330

Gwamnatin jihar Oyo ta bayar da wa’adin mako guda ga masu shagunan da aka gina a shingen makarantun gwamnati a jihar da su rusa shagunan tare da dakatar da duk wasu harkokin kasuwanci.

Gwamna Seyi Makinde wanda ya yi wannan gargaɗin a jiya jim kaɗan bayan ya duba wasu makarantun gwamnati a Ibadan, ya bayyana cewa gwamnati za ta kawo hayyacinta a muhallin makarantar gabanin komawar ɗalibai.

Gwamnan wanda ya ci gaba da cewa gwamnati na da aniyar ganin an samar da yanayin koyo a jihar, ya koka kan halin da ake ciki na koyo da harkokin kasuwanci da ke kusa da shiga makaranta.

Ya kuma lura da yadda ake tafiyar da sharar gida a faɗin babban birnin jihar, inda ya ce gwamnati za ta fito da tsare-tsare don ganin muhalli ya zama abin alfahari ga kowa.

KU KUMA KARANTA: Wike ya ba da umarnin rusa gidajen kwana a ‘Kabusa junction’

Ya ce: “Kusan mutanen da shagunansu ke daf da ƙofar shiga makarantar, sun rufe kofar shiga, wanda ba shi da amfani wajen koyo.

Don haka, mun zagaya, abin da muke cewa shi ne, idan kana da wani abu da aka maƙala a katangar makaranta, sai ka cire shi.

“Za mu ba su kusan mako guda don cire waɗannan abubuwan. Su share su ta yadda idan yaranmu suka dawo makaranta, mu san sun shigo cikin yanayin da ya dace da koyo.

Leave a Reply