Jihar da ta fi yawan ‘yan gudun hijira a Najeriya – NBS
Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce aƙalla mutum 1,134,828 daga iyalai 251,082 ne suke gudun hijira a cikin gida Najeriya a shekarar 2023.
Wani rahoto kan ‘Yan Gudun Hijira na Cikin Gida na 2023 da NBS ta fitar a ranar Litinin da marece, ya nuna cewa jihar Borno ce ta fi yawan ‘yan gudun hijirar inda 206,753 daga cikin jumullar adadin suka kasance nata.
A jihar Borno kadai, mutum 877,299 ne suka rasa matsugunansu inda suke gudun hijira a cikin gida, waɗanda yawansu ke wakiltar kashi 77.3 na daukacin mutanen da aka yi binciken a kansu.
Ya bayyana cewa an gudanar da binciken ne a shekarar 2023 a fadin jihohi bakwai da suka hada da Adamawa da Yobe da Borno da Sokoto da Katsina da Benue da kuma Nasarawa.
“Binciken ya nuna cewa rikicin Boko Haram shi ke da alhakin saka kashi 81.2 cikin 100 na yawan mutanen da ke gudun hijirar, rikicin manoma da makiyaya ya saka kashi 16.2 cikin 100. matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane ta saka kashi 1.6 bisa 100.
KU KUMA KARANTA: Cin zarafi ta hanyar lalata ya ƙaru a ƙasar Haiti ; Rahoto
“Wannan yana nuna cewa matsalar da ɗan’adam ke jawo wa mutum ɗan’uwansa ta fi haifar da gudun hijira fiye da ambaliyar ruwa ko sauran nau’ikan na bala’i.”
Rahoton ya bayyana cewa gudun hijira na cikin gida na mutane shi ne motsi na tilastawa mutane a cikin kasarsu saboda rikici, tashin hankali, bala’o’i, ko wasu rikice-rikice, ba tare da ƙetare iyakokin ƙasa da ƙasa ba.
A cewar rahoton, wannan ya kasance daya daga cikin matsalolin jinƙai da suka fi daukar hankali a Najeriya, saboda gudun hijirar ya samo asali ne sakamakon wasu manyan matsaloli.
Matsalolin sun hada da rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas da na ‘yan fashi da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma da rikicin ‘yan bindiga da kuma rikicin ƙabilanci a wasu sassan ƙasar.
Ƙarin bincike ya nuna cewa a cikin jimillar yawan mutanen da aka yi nazari a kansu, kashi 50.3 cikin 100 ƙanana ne kuma ba su kai shekaru 18 ba.
Kashi 49.7 ne kawai ke tsakanin shekaru 18 zuwa sama. Duk da haka, an lura cewa kashi 83.4 na mutanen sun yi gudun hijirar ne a cikin shekaru hudu.