Jarumar Kannywood Maryam Muhammed ta roƙi kotu ta raba auren ta da mijinta
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Lauyan jarumar, A.S Ibrahim, ya shaidawa kotu cewa wanda ake ƙara ya yi furucin saki na uku shekaru biyar da suka gabata bayan da ta nemi saki ta hanyar Khul’i (haƙƙin mace a Musulunci na neman saki tare da dawo da sadakin da aka bata).
“Ya yi furucin saki sau biyu bayan da mai karar ta shigar da kara a kotu tana neman saki ta hanyar Khul’i.
“An kai masa sammaci daga kotu, kuma ya rubuta saki na uku a kan takardar sammaci, wanda mai karar ta karanta sannan ta ci gaba da rayuwarta ba tare da ta sake komawa kotu don tabbatar da sakin ba,” in ji lauya.
KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai ta ba da horo ga mata 50 don su zama daraktoci a Kannywood
Sai dai wata majiya ta rawaito cewa, wanda ake kara bai halarci zaman kotun a wannan rana ba, kuma bai aika da wakili ba.
Alkalin kotun, Kabir Muhammad, ya tambayi mai kai sammaci ko ya isar da takardar ga wanda ake kara, sai ya ce bai same shi a gida ba.
Alkalin ya umarci jami’an kotu da su mika takardar sammaci ta wata hanya ta daban sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 27 ga Fabrairu.