Jaridar Almizan ta karrama Dakta Yusuf Ali, Farfesa Gwarzo, Media Trust, Ibrahim Musa da Mawaƙi Saƙafa Potiskum

0
24
Jaridar Almizan ta karrama Dakta Yusuf Ali, Farfesa Gwarzo, Media Trust, Ibrahim Musa da Mawaƙi Saƙafa Potiskum

Jaridar Almizan ta karrama Dakta Yusuf Ali, Farfesa Gwarzo, Media Trust, Ibrahim Musa da Mawaƙi Saƙafa Potiskum

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kamfanin Mizani Publication Ltd, masu wallafa jaridar Almizan ta karrama mutane biyar saboda gudumawar da suke bai wa al’umma ta fuskoki daban-daban.

Jaridar ta yi wannan karramawar ne a yayin da take bukin shekaru 35 da kafa jaridar wanda ya gudana a birnin Kano a ranekun 10 zuwa 12 ga watan Janairun 2025.

An karrama waɗannan zaƙaƙurai ne a yayin rufe taron a ranar Lahadi 12 ga Janairun 2025 a ɗakin taro na Mambayya House da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.

Jaridar ta soma karrama Malam Ibrahim Musa, babban Editan Almizan tun lokacin da aka kafa ta, saboda irin gudumawar da ya bayar na isar da saƙonni da ganin ɗorewarta har ya zuwa yau. Inda ya karɓi karramawar ta shi tare da tawagarsa dake ɗauke da ma’aikatan jaridar.

Kazalika, ta kuma karrama Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya assasa rukunin jami’o’in MAAUN ta jamhuriyar Nijer da Nijeriya, FBIU, Canadian University, da kuma irin gudummawar da ya bai wa ‘yan jarida a lokacin da yake riƙe da shugabancin ƙungiyar kare haƙƙin ‘yan jarida ta Afrika da kuma irin gudummawar da yake bai wa ɓangaren ilimi a Nijeriya da ma nahiyar Afrika baki ɗaya. Shugabannin jami’o’in MAAUN Nijeriya, da kuma FBIU Kaduna, Farfesa Mohammad Israr da Farfesa Abdullahi Muhammad Sabo ne suka karɓi karramawar a madadinsa.

KU KUMA KARANTA: An karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano

Har wala yau jaridar ta karrama Marigayi Dakta Yusuf Ali, saboda irin gudummawar da ya bai wa jaridar na tsawon lokaci. Inda ‘ya’yansa Malam Musbahu, da Dakta Bilkisu Yusuf Ali, Malama a jami’ar Alƙalam da ke Katsina suka karɓi karramawar a madadin mahaifinsu.

Jaridar har wala yau ta karrama kamfanin Media Trust, mawallafan jaridar Daily Trust, Aminiya, Trust Radio, da kuma Trust TV, saboda irin haɗin kan da suka bai wa jaridar Almizan a tsawon shekaru 14 da suke hulɗa. Malam Naziru Mika’il wanda tsohon Darakta ne a Media Trust ɗin shi ne ya bai wa wakilin Daily Trust a Kano karramawar a madadin jaridar Almizan.

Jaridar ALMIZAN, ba ta yi ƙasa a guiwa ba, ta karrama Malam Saidu Sakafa, shahararren mawaƙin Shuhada’u daga garin Potiskum saboda irin gudummawar da yake bai wa jaridar ta hanyar waƙe jaridar a tsawon lokaci. Mawaƙin ne tare da tawagarsa ya karɓi karramawar.

Waɗanda aka karrama sun bayyana jin daɗin su bisa karramawar da jaridar ta yi musu. Inda suka yi wa jaridar fatan alheri da addu’ar ci gaba da samun karɓuwa da ɗaukaka a tsakanin al’umma.

A yayin taron wanda aka kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanarwa, an gabatar da jawabai daban-daban daga Malamai, masana, ‘yan jarida, da sauran su. Kuma taron ya samu halartar wakilai da ma’aikatan jaridar daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply