Jam’iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaɓen jihar Edo

0
95
Jam'iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaɓen jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaɓen jihar Edo

A ranar Lahadi, hukumar INEC ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Edo, nasarar da PDP ta ke ƙalubalanta.

Jam’iyyar PDP ta yi ƙira ga Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Jihar Edo.

A ranar Asabar al’umar jihar wacce ke kudu maso kudancin Najeriya suka kada kuri’unsu a zaɓen.

A ranar Lahadi, hukumar INEC ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

KU KUMA KARANTA: Ba zan yi wa kowa takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba — Obi

Sai dai jam’iyyar ta PDP ta nemi INEC da ta sake duba sakamakon tana mai cewa bai nuna asalin yadda al’umar jihar suka kada kuri’unsu ba.

Muƙaddashin Shugaban jam’iyyar ta PDP a wani taron manema labarai a Abuja, Ambasada Umar Damagum, ya ce jam’iyyar za ta ƙalubalanci zaɓen a kotu.

Damagum ya bayyana cewa mutanen Edo Dr. Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP suka zaba a matsayin gwamna na gaba, yana mai cewa dole a bar zabinsu da suka bayyana a rumfunan zabe.
“Za ku iya tunawa cewa PDP ta sha jan hankali kan kitse-kitsen da APC ta yi na ganin ta murde zaben.”

“A dalilin haka, jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Gwamna na jihar Edo, saboda bai da sahihancin da tsarin dimokradiyya ya tanada.

“PDP na ƙira ga hukumar zaɓe ta INEC da ta sake duba sakamakon zaɓen jihar Edo kamar yadda dokar zaɓe ta sashe 65 ta shekarar 2022 ta ba ta dama, in ji Damagum.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba ya garzaya kotu.

“Shugaba Tinubu na ƙira ga waɗanda ba su gamsu da sakamakon zaɓen ba da su bi ta hanya da doka ta tanada don neman hakkinsu.” Onanuga ya ce.

Okpebholo na APC ya samu ƙuri’u 291,667. Sai ɗan takarar jam’iyyar PDP Asue Ighodalo wanda ya samu ƙuri’u 247,655.

Olumide Akpata, na jam’iyyar Labour Party (LP), ya kammala a matsayi na uku, inda ya samu ƙuri’u 22,763.

Leave a Reply