Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Kawu Sumaila, Rurum da Ali Madaki
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu mambobinta, ciki har da sanata da ‘yan majalisar dokoki, bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa manufofin jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin.
KU KUMA KARANTA:Majalisar Malamai ta jihar Kano ta yanke hukunci kan rikicin masallacin Bin Uthman da ke Kundila
Ya ce, daga cikin ‘yan majalisar da abin ya shafa akwai Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, Alhaji Abdullahi Sani Rogo, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo, Alhassan Rurum mai wakiltar Rano/Kibiya, da kuma Ali Madakin Gini mai wakiltar mazabar Dala a majalisar wakilai.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa, jam’iyyar ta nuna rashin jin dadinta kan halayen wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar.
A cewarsa, duk da cewa jam’iyyar ta ba su tikitin takara kyauta a lokacin zabe, wasu daga cikinsu sun aikata abubuwan da su ka saba da manufofi, ka’idoji da kuma tsarin jam’iyyar.