Jami’ar Ahmadu Bello ta karrama Dakta Kera, Dakta Hauwa Sani da wasu 121 (Bidiyo)

0
6
Jami'ar Ahmadu Bello ta karrama Dakta Kera, Dakta Hauwa Sani da wasu 121 (Bidiyo)
Dakta Hauwa Sani tare Dakta Kera

Jami’ar Ahmadu Bello ta karrama Dakta Kera, Dakta Hauwa Sani da wasu 121 (Bidiyo)

Daga Idris Umar, Zariya

Ma’aikata 123 jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ba lambar girmama a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairun shekarar 2025 domin fice da suka yi wajen bayar da gudummuwarsu wajen cigaban jami’ar a ɓangarori daban daban.

Wakilinmu ya samu halartar taron wanda ya gudana a ƙarƙashin jagorancin shugaban jami’ar, Farfesa Kabiru Bala.

Wannan dai shine karo na biyu da jami’ar ta gudanar da irin wannan taron tun bayan kafa tsarin da ke kula da ƙoƙari da kuma jajircewa a kan aiki domin a samar da wani yanayin aiki mai kyau ga dukkan ɓangarorin ma’aikatan jami’ar baki ɗaya.

A shekarar da ta gabata, ma’aikata 117 aka girmama bayan ganin irin kokarin da suka nuna domin kara kwarin gwiwa ga ma’aikatan jami’an baki ɗaya.

 

Dakta Kera yayin karɓar kyautar girmamawa

Kwamitin da ke kula da bayar da shaidar girmamawa wanda kuma shi ke kula da kokarin da ma’aikatan ke yi a makon da ya gabata ya bayar da rahotonsa ga hukumar jami’ar inda ya ke nuni da bayar da lambobin girmamawa daban-daban har 26 ga ma’aikata 123.

Dakta Hauwa Sani yayin karɓar kyautar girmamawa

Yayin bayar da shaidar girmamawar, kwamitin ya bi tsarin da aka samar na bayar da lambar girmamawar kamar yadda jami’ar ta tanada.

Aikin kwamitin har wa yau ya yi daidai da matakan da akan bi wajen tantance ma’aikatan da suka yi aiki tukuru ga jami’ar a matakai daban-daban.

KU KUMA KARANTA: Jamiar NOUN za ta ba Hafsatu Abdulwaheed da Innocent Chukwuma digirin girmamawa

Wannan aiki an yi shi ne bisa nuna dacewar bayar da lambobin girmamawar da cibiyoyi daban-daban suka mika kuma suna nuna cewa ya dace a bayar da su ga ma’aikatan kamar yadda aka tsara da kuma bayanan da sauran mutanen da ke jami’ar suka bayar ta hanyar amsa tambayoyin da aka yi masu a rubuce.

Wasu daga cikin wadanda aka mika sunayen nasu domin basu shaidar girmamawar da kuma nuna an kula da irin jajircewar da suka yi na shekarar 2024 sun hada da Farfesa Muhammad Habibu Sabari daga ɓangaren ABU Business School, sai Farfesa Aisha I. Mamman daga Sashen Faculty of Basic Clinical.

Dakta Hauwa Muhammed Sani itace mataimakiyar shugaban IDR na jami’ar kuma tana daya daga cikin wadanda aka girmama, yayin da ta ke zantawa da wakilinmu ta ce wannan girmamawa ya sa ta ji dadi sosai kuma ya kara ma ta kwarin gwiwa wajen nuna kwazo a wajen aikin ta, bisa haka ta yi kira ga sauran ma’aikata manya da kanana cewa su dage da yin aiki tukuru da yin gaskiya a wajen aiki, hakan zai sa su samu nasara, inda ta yi yabo ga shugaban jami’ar musamman yadda ya ke bayar da gudummawarsa wajen cigaban ilimi.

A ƙarshe ta yi jinjina ga kwamitocin da suka zauna suka gudanar da wannan muhimmin aiki, ta yi fatan Allah Ya taimaki jami’ar Ahmadu Bello, jihar Kaduna da Nijeriya baki ɗaya.

A yayin da ya ke rufe taron, Farfesa Kabiru Bala ya nuna jin daɗin shi ga dukkanin wadanda suka samu lambar girma kuma wadanda ba su samu ba su ma su yi aiki tukuru domin su ma su kasance cikin wadanda za su samu lambar girmamawar a nan gaba.

Daga cikin manyan dattijan da suka halarci wannan taro akwai tsohon ministan gona, Sheikh Abdallah Dangi da Alhaj Malam Abba Bello.

Ga bidiyon hirar su da wakilinmu

Leave a Reply