Jami’an tsaron Najeriya sun ceto ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka guda biyu da aka sace

Jami’an tsaro sun ceto wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Ogbaru da ke Anambara a ranar 16 ga watan Mayu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambara DSP Tochukwu Ikenga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a garin Awka a ranar Juma’a, inda ya ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun ceto mutanen biyu da sanyin safiyar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi wa ayarin jami’an ofishin kwanton-ɓauna a ranar Talata, inda suka kashe mutane bakwai ciki har da ‘yan sanda, sannan suka yi awon gaba da biyu.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun halaka ƴan bindiga da ƙwace makamansu da babura a Kaduna

Haka kuma an ƙona gawarwakin waɗanda aka kashe a hanyar Atani zuwa Osamala a Anambara.

Mista Ikenga ya ce jami’an tsaro sun ci gaba da gudanar da aikin tsaro a yankin.

Kakakin ‘yan sandan ya ce za a yi ƙarin bayani ga jama’a kan aikin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *