Jami’an tsaro sun tarwatsa sansanonin ɓarayin daji da dama

0
30
Jami'an tsaro sun tarwatsa sansanonin ɓarayin daji da dama

Jami’an tsaro sun tarwatsa sansanonin ɓarayin daji da dama

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da tarwatsa sansanonin ɓarayin daji da dama da kuma ƙwato makamai a Jihar Taraba.

Muƙaddashin mataimakin mai magana da yawun Rundunar Sojin, Olubodunde Oni ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Jalingo inda ya bayyana cewa sojojin Birget ta shida ƙarƙashin rundunar Operation Whirl Stroke ne suka gudanar da aikin.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Kingsley Uwa inda suka kutsa maɓoyar ‘yan ta’adda da dama a Taraba.

Sanarwar ta bayyana cewa a yayin wani samame da suka kai a ranar 28 ga Nuwamban 2024 a Ƙaramar Hukumar Takum, an lalata maɓoyar ‘yan ta’dda inda sojojin suka gano harsasai 27 da bindigar AK 47 ɗaya da wata wayar oba-oba da babura biyu.

“Domin tabbatar da tsaron mazauna yankin, an ajiye dakaru a yankunan Akume da Ananum da ke Ƙaramar Hukumar Donga a ranar 30 ga Nuwamban 2024 domin nuna yadda sojojin ke mayar da hankali wurin kare rayuka da dukiyoyi a faɗin Jihar Taraba.”

KU KUMA KARANTA: Jamian tsaro sun kama ;yan bindiga 3 da mai yin safarar makamai

A ‘yan kwanakin nan rundunar sojojin Nijeriyar na yawan sanar da irin nasarorin da take samu a yaƙin da take yi da ‘yan ta’adda musamman a arewa maso gabashin ƙasar da kuma arewa maso yamma.

Ko a makon da ya gabata sai da sojojin suka sanar da kashe ‘yan ta’addan ISWAP 12 a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Leave a Reply