Jami’an tsaro a Benuwe sun lalata maɓoyar ’yan bindiga
Rundunar Sojin Operation Golden Peace, sun kai samame tare da samun nasarar lalata maɓoyar ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Benuwe.
Rundunar Sojin Operation Golden Peace, sun kai samame tare da samun nasarar lalata maɓoyar ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Benuwe.
Sojojin sun kai farmaki maɓoyar ’yan bindigar a ƙauyukan Akahagu, China, da Ikayor, inda suka kai hari kan sansanin wani da ake nema mai suna Akiki Utiv, wanda aka fi sani da “Full Fire.”
KU KUMA KARANTA: Jamian tsaro sun tarwatsa sansanonin ɓarayin daji da dama
A yayin samamen, sojojin sun ƙwato wata mota ƙirar Toyota Corolla, babur, bindiga, harsashi da kuma wandon sojoji.
Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba da jarumtar sojojin tare da buƙatar jama’a su riƙa bayar da bayanai masu amfani domin tallafa wa hukumomi.
Har ila yau, ya jadadda ƙoƙarin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da kare lafiyar al’umma.