Iyayen ‘yan matan Chiɓok sun roƙi Tinubu da ya taimaka a sako musu sauran ‘ya‘yansu 92

0
297

Iyayen ‘yan matan Chibok da ke cikin damuwa sun roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya taimaka wajen ganin an sako ‘yan matan 92 da har yanzu suke hannun Boko Haram.

Iyayen sun yi wannan roƙo ne a wata takarda da Yana Galang (mahaifiyar Rifkatu Galang da har yanzu take tsare) da Zanna Lawan (mahaifin Aisha Lawan) suka fitar ranar Litinin.

Sun kuma taya Tinubu da Kashim Shettima murnar samun muƙamin shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa.

Sun roƙi shugaban ƙasar da ya yi amfani da ofishinsa mai daraja wajen taimakawa a sako sauran ‘yan matan da ake tsare da su.

KU KUMA KARANTA: An sake ceto ƴan matan Chibok biyu a Jihar Borno

“Shugaban ƙasa, kamar yadda ka sani, matsalarmu ta faro ne tun a shekarar 2014 lokacin da aka sace ‘ya’yanmu mata 276 daga makarantar sakandaren gwamnati ta Chiɓok.

“Shekaru ne na zafi da raɗaɗi a gare mu, kuma mun ji takaicin cewa bayan shekaru tara da ‘yan watanni kafin ƙarshen gwamnatin da ta shuɗe, 92 daga cikin waɗannan ‘yan matan sun ci gaba a riƙe a hannun ‘yan Boko Haram, inda suka fuskanci wahala da cin zarafi da ba za a iya misaltuwa ba hannun waɗanda suka yi garkuwa da su,” in ji iyayen.

Iyayen, a cikin wasiƙar sun amince da cewa, Tinubu a jawabinsa na ƙaddamarwa, duk da cewa bai yi alƙawari kai tsaye ba musamman kan halin da suke ciki a Chiɓok, ya yi alƙawarin ba da fifiko kan tsaro.

Daga bisani sun nemi kulawar shugaba Tinubu don ba da haske don gano sauran 92 na ‘yan matan da aka sace.

A cewar iyayen, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a jawabinsa na ƙaddamarwa a ranar 29 ga watan Mayu, 2015, ya ce gwamnatinsa ba za ta iya iƙirarin murƙushe Boko Haram ba, ba tare da ceto ‘yan matan Chiɓok ba.

Sun ƙara da cewa a ranar 14 ga Afrilu, 2021, an fitar da wata sanarwa mai taken “Yan matan Chiɓok har yanzu suna kan hankalinmu” tare da ƙara tunatar da su alƙawarin da tsohon shugaban ƙasar ya yi tare da tabbatar musu da cewa za a kuɓutar da dukkan ‘yan matan nasu tare da mayar da su cikin yankunansu.

“Yayin da sanda ta canza a karkashin jam’iyyar siyasa ɗaya a yanzu a 2023, babu shakka tarihi zai yi kyau a gare ku, dangin ku, gwamnatin ku da jam’iyyar ku idan an cimma waɗannan kalamai na magabata a ƙarƙashin ku, fiye da haka, tare da ɗanmu, mataimakin shugaban ƙasa, Shettima.

“Mai girma shugaban ƙasa muna neman ka ne ka zame mana hasken da zai haskaka duhun mu, ya kawo ƙarshen raɗaɗin da muke ciki, ya share mana hawaye, ya ‘yantar da mu daga ƙangin baƙin ciki, da ƙuncin rayuwa da wannan yanayin ya kawo mu.

“Lokacin da muka cika shekara tara da tunawa da sace ‘ya’yanmu a bana, ba ma fatan mu sake yin bikin ba tare da ‘ya’yanmu ba. Ku cece mu, ku taimake mu waɗannan yara su fito a mulkinku.

“Muna jira, muna ƙara haƙuri don wannan taimakon a matsayin madadin mu,” in ji iyayen.

Leave a Reply