Iyayen ‘yan makarantar Yauri da ke hannun masu garkuwa da mutane sun fara tara kuɗin fansa naira miliyan 100

Iyayen ragowar ɗalibai ‘yan mata 11 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke garin Yauri a Jihar Kebbi, sun shiga wani shiri na tara kuɗin fansa Naira miliyan 100 domin a sako ‘ya’yansu.

A ranar 17 ga watan Yunin 2021 ne aka sace ɗalibai sama da 80 a lokacin da wasu ‘yan bindiga ƙarƙashin jagorancin wani da ke kira Sarki Dogo Gide suka kai hari makarantar.

Daga baya an sako yawancin ɗaliban ga gwamnatin jihar bayan an biya kuɗin fansa, sai dai bayan watanni 19 ‘yan ta’addan sun ci gaba da tsare 11 daga cikin ɗaliban, inda suke neman kuɗin fansa Naira miliyan 100 akan su.

A hirar da jaridar Daily Trust tayi da iyayen yaran a ranar lahadi, iyayen ɗaliban da aka sace da suka haɗu a harabar makarantar sun koka kan yadda gwamnati ta ƙi ɗaukan mataki, shine suka yanke shawarar ɗaukan mataki da kansu.

KU KUMA KARANTA:Sojoji sun kuɓutar da ‘yar makarantar Chibok a Borno, bayan shekara takwas da saceta

Shugaban ƙungiyar iyayen, Salim Kaoje, ya bayyana cewa sun ƙulla alaƙa da Dogon Gide tare da taimakon mahaifiyar shi, wadda ya ce tana ƙara matsa masa lamba kan ya sako ‘yan matan.

“Mun ƙulla alaƙa da Dogo Gide ne a ranar 15 ga watan Disamban 2022, da farko ya ƙi amincewa da duk wani yunƙurin tattaunawa da mu, amma bayan da mahaifiyarsa ta shiga tsakani, ya amince ya sako yaran mu idan muka biya kuɗin fansa naira miliyan 100, ko kuma ba za mu taba ba ganin ‘ya’yanmu ba, idan bamu biya ba.

“Ya bayyana ƙarara cewa idan har ba mu cika sharaɗin da ya bamu ba, ba za mu sake gani ko jin ta bakin ‘ya’yanmu ba, kuma wannan ne ya sa muka taru a matsayin iyaye domin yin wannan roko,” inji shi.

Kaoje ya ce kowanne daga cikin iyayen ya ƙuduri aniyar sayar da duk wani abu da ya mallaka da suka haɗa da kadarorin ƙasa da sauran kayayyaki masu daraja, domin samun damar tara ƙuɗin.

Wani uba mai suna Umar Abdulhamid ya ce matakin ya zama dole saboda sun yi watsi da gwamnati.

“Kusan shekara guda kenan da wata takwas da sace yaran mu, mun jira gwamnati, amma kamar ba su son yin komai don ganin sun dawo lafiya,” inji shi.

Wata mahaifiyar ɗaya daga cikin ‘yan matan mai suna Serah Musa, ta ce ba su da wani zaɓi da ya wuce su fito cikin jama’a tunda gwamnati ta yi watsi da su.

“Ba mu sami kanmu ba tun lokacin da abin ya faru, kuka muka yi har ta kai ga mun daina zubar da hawaye.

“Waɗannan yaran sun yi ƙanƙanta da za a bar su a hannun ‘yan fashi, saboda babba a cikinsu ‘yar shekaru 16 kacal,” in ji ta.

Don haka ta bukaci ‘yan Najeriya da su taimaka musu wajen tara kuɗin fansa domin ganin an sako ‘ya’yansu.


Comments

One response to “Iyayen ‘yan makarantar Yauri da ke hannun masu garkuwa da mutane sun fara tara kuɗin fansa naira miliyan 100”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Iyayen ‘yan makarantar Yauri da ke hannun masu garkuwa da mutane sun fara tara kuɗin fansa naira … […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *