Isra’ila tana shirin kai farmaki a wani sansanin ‘yan gudun hijira a Gaza

0
98
Isra'ila tana shirin kai farmaki a wani sansanin 'yan gudun hijira a Gaza

Isra’ila tana shirin kai farmaki a wani sansanin ‘yan gudun hijira a Gaza

Yau Asabar ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ba da umarni kwashe mutane daga wani wuri mai tarin jama’a a Gaza inda aka keɓe domin gudanar da ayyukan jin ƙai.
Ma’aikatar ta faɗa cewa tana shirin kai farmaƙi a kan mayaƙan Hamas a Khan Younis, da wani ɓangaren Muwasi da aka tsugunar da dubban ‘yan gudun hijira.

Umarnin ya biyo bayan martani da Isra’ila ta bayar kan wani makamin roka da ta ce an harbo ne daga wurin.

Umarnin kwashe mutanen shi ne na biyu a cikin mako guda daga wurin da aka keɓewa Falasɗinawa da suka tsere daga wasu sassan Gaza. Sau tari ana ta da Falasɗinawa da dama da suke neman mafaka daga farmaki ta sama da ƙasa da Isra’ila ke kaiwa.

KU KUMA KARANTA:‘Yan Houthi na Yaman sun kai hari kan jiragen ruwan Isra’ila da Amurka da Birtaniya 102 a rikicin Gaza

A ranar Litinin jim kaɗan bayan umarnin ta da mutanen, hare-hare da dama da Isra’ila ta kai ta sama a gewayen Khan Younis ya kashe aƙalla mutane 70, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, tana nuni da wasu alƙalumar da asibitin Nasser ya fitar.

Wannan ɓangaren yana cikin yanki mai girmar murabba’in kilomita 60 wanda aka keɓe domin gudanar da ayyukan jin ƙai, wanda Isra’ila ta yita fadawa Falasdinawa su tashi daga wurin tun farkon yaƙin.

An yi amfani da wani bangare mai girma na yankin aka kafa dakunan tanti wanda ba su da kayayyakin tsafta kana ba asibitotci sannan ba su samun isasshen taimakon jin kai, a cewar MDD da kungiyoyin jin kan.

Kimanin Falasdinawa miliyan guda da dubu 800 ne suke tsugune a wurin a cewar wani kiyasin Isra’ila. Wannan adadin ya kai rabin al’ummar Gaza, mai mutane miliyan 2 da dubu 300 kafin yakin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here