Isra’ila ta kashe fararen hula 2 da jikkata mutane da dama a Gaza

0
51
Isra'ila ta kashe fararen hula 2 da jikkata mutane da dama a Gaza

Isra’ila ta kashe fararen hula 2 da jikkata mutane da dama a Gaza

Dakarun Isra’ila sun kashe fararen-hula biyu tare da jikkata wasu bayan sun jefa bama-bamai a wani gida da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA.

Rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce ta ɗauko gawa biyu da kuma mutanen da suka jikkata daga gidan iyalan Araj da ke Jalaa Street bayan Isra’ila ta kashe su.

Daga bisani adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 11 bayan jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a Makarantar Safad da ke kudu maso gabashin Gaza, inda ‘yan gudun hijira suke fakewa.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta bai wa Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu – MƊD

Ma’aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, yayin da Isra’ila ke barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin.

Leave a Reply