Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 14 a sabbin hare-hare da ta kai a Gaza
Isra’ila ta kai ƙarin hare-hare a faɗin yankin Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 14, 10 daga cikinsu a gida ɗaya a Birnin Gaza, kamar yadda ma’aikatan kiwon lafiya suka bayyana.
Hakan na faruwa ne a yayin da dakarun Isra’ila suke ci gaba da kutsawa kudancin Rafah.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun ce dakarun Isra’ila sun kai hari a wani gida a unguwar Daraj da ke wajen Birnin Gaza inda suka lalata shi tare da gidajen da ke kusa da shi.
Kazalika dakarun na Isra’ila sun kashe mutum huɗu a hare-hare biyu da suka kai ta sama a birnin da kuma garin Beit Lahia da ke arewacin yankin, in ji ma’aikatan kiwon lafiya.
Kawo yanzu rundunar sojojin Isra’ila ba ta ce uffan ba game da waɗannan hare-hare.
A yankin Rafah, kusa da kan iyaka da Masa, tankokin yaƙin Isra’ila sun ci gaba da kutsawa inda suka nufi yankin Mawasi da ke yammaci, wanda ana ayyana a matsayin tudun-mun-tsira.
KU KUMA KARANTA: Harin da Isra;ila ta kai a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama
Sun riƙa buɗe wuta a yayin da suke tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa arewaci inda Khan Younis yake.