Isra’ila ta kama mutum 15 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

0
53
Isra'ila ta kama mutum 15 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Isra’ila ta kama mutum 15 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

Aƙalla Falasɗinawa 15 Isra’ila ta ƙara kama a wani samame da ta kai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, kamar yadda wata ƙungiya da ke kula da fursunoni ta tabbatar a ranar Lahadi.

Sojojin sun kai samamen ne a Hebron da Tubas da Ramallah da Birnin Kudus, kamar yadda hukumar da ke kula da waɗandake tsare da kuma ƙungiyar kula da fursunoni Falasɗinawa suka bayyana a wata sanarwa ta haɗin gwiwa.

KU KUMA KARANTA: Hezbollah ta harba rokoki 200 da jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

“Waɗanda aka kama na fuskantar cin zarafi da duka, da kuma barazana ga iyalansu, baya ga yawaitar ayyukan zagon kasa da lalata gidajen ‘yan ƙasar,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Kamen na ranar Lahadi ya kawo adadin Falasɗinawa da Isra’ila ta kama tun daga 7 ga watan Oktoba a Yammacin Kogin Jordan zuwa 9,550 a cewar alkaluman Falasɗinawa.