Isra’ila ta bai wa Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu – MƊD
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana girman mamayar da sojojin Isra’ila suke yi wa yankin Gaza, tana mai cewa an kori kusan kashi 84 daga yankin.
Da yake bayani kan alƙaluman da Ofishin Babban Mai Kula da Harkokin Jinƙai na Majalisar (OCHA) ya tattara, mataimakin kakakin ofishin Farhan Haq ya shaida wa manema labarai cewa “luguden wuta da kuma kutsen da Isra’ila take yi a Gaza na ci gaba da kashewa da jikkatawa tare da korar Falasɗinawa daga matsugunansu, da kuma rusa gidajensu da sauran gine-gine da suka dogara a kansu.”
Ya ce, “Sau biyu sojoji suna bayar da umarni ga mutane su fita daga Khan Younis a ƙarshen mako, zuwa yankunan da a baya galibi aka umarci mutane su fice daga cikinsu.”
KU KUMA KARANTA: Dubban Falasɗinawa sun tsere daga wani yanki a tsakiyar Gaza
Wannan lamari ya shafi yankuna 23 da wurare 14 da ke samar da ruwa da tsaftar jama’a da kuma makarantu huɗu.
“Jimilla, sojojin Isra’ila sun kori mutane daga wurin da ya kai girman murabba’in kilomita 305, wato kusan kashi 84 na yankin Zirin Gaza,” in ji shi.