Ƙasashe da dama da ƙungiyoyi masu zaman kansu a faɗin duniya na caccakar Isra’ila kan kashe ma’aikatan agaj na ƙungiyar World Central Kitchen a Gaza.
Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ransa ya ɓaci matuƙa kan kisan ma’aikatan. Ƙasar Canada a nata ɓangaren, ta yi Allah wadai da kisan sojojin inda ta buƙaci a gudanar da bincike.
Ita ma ƙasar Jamus a ranar Talata ta buƙaci Isra’ila ta gudanar da bincike mai zurfi kan kisan ma’aikatan.