INEC ta fitar da farashin tsayawa takara na zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

0
80
INEC ta fitar da farashin tsayawa takara na zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

INEC ta fitar da farashin tsayawa takara na zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Daga Idris Umar, Zariya

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kano (KANSIEC) ta sanya Naira Miliyan 10 ga ‘yan takarar da ke neman kujerar Shugaban ƙaramar Hukuma, yayin da ƴan takarar kansiloli za su biya Naira miliyan 5 gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Shugaban INEC (KANSIEC) ta Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana haka a yayin gabatar da ƙa’idojin zaɓe da jadawali ga wakilan jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa ɗan takarar da zai tsaya takarar shugaban ƙaramar hukuma dole ne ya biya Naira miliyan 10 don samun tikitin zaɓen, yayin da ɗan takarar kansila zai biya Naira Miliyan 5.

Malumfashi ya bayyana cewa ƙa’idojin sun bayyana dukkan batutuwan da suka shafi cancanta da kuma rashin cancanta na masu takara.

Ya ce, ƙa’idojin sun ƙunshi abin da bai kamata a yi ba a lokacin zaɓen, yana mai gargaɗin cewa duk wata jam’iyya ko ɗan takarar da aka samu da aikata magudin zaɓe zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Wani ɓangare na ƙa’idojin a cewarsa shi ne masu neman kujerar ƙananan Hukumomi dole su kasance masu shekaru 30 zuwa sama.

Masu neman takarar kansila kuwa ya bayyana cewa dole ne su kasance masu shekaru 25 zuwa sama, da haka ya ƙara da cewa dole ne dukkansu su kasance sahhalallun ƴan jam’iyyun siyasa a jam’iyyar su.

Dole ne masu neman kujerar ƙananan Hukumomi su kasance basu cikin yayin fuskantar yawan bashi ko fatara, ko kuma aka taɓa tsarewa a gaban hukuma, Dole ne su kasance cikin koshin lafiya ta jiki da ta ƙwaƙwalwa, kuma su sami akalla takardar shaidar kammala Sakandare.

“Dole ne ga Duk masu neman Takara da kada su kasance masu shaye-shayen miyagun kwayoyi ko mambobin kungiyoyin asiri,” inji shi.

Malumfashi ya kuma bayyana cewa za a fara yakin neman Zaɓen a ranar 6 ga watan Satumba, kuma za a kammala ranar 31 ga watan Oktoba yana mai kira ga jam’iyyun siyasa da su tabbatar da gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe cikin lumana.

Ya ce “A lokacin yakin neman zabe muna gargadi game da batanci da kalamai na cin mutumci, da kai hare-hare a lokacin yakin neman Zaɓe, duka waɗannan suna cikin ka’idojin.

KU KUMA KARANTA:INEC ta dakatar da wani jami’inta don gudanar da bincike kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a

Dole ne ku kasance masu hakuri da juna, Ku kasance cikin lumana bisa tsarin dimokuradiyya, a cikin yakin neman zaben haka ya kamata ba a fito ana sukar juna ba.

Muna da matsalolin da suka addabi kasar nan kamar su samar da ababen more rayuwa, da magance talauci, da tallafawa Matasa, da tallafawa kungiyoyin marasa galihu da sauran su ne ya kamata ku yi amfani da su a yayin yakin neman zabe.

Ba za mu lamunci tashin hankali ba saboda ya saba wa dokokin zabe, mun hana kai hare-hare na zahiri ko na kalamai a zaben kuma za mu yi hukunci bisa doka.”

Shugaban ya kuma jaddada cewa ba zai lamunci cin hanci da rashawa a lokacin zaɓen ba, kuma duk wanda ya yi yunkurin ba shi cin hanci to zai tona masa asiri tare da hukunta shi.

Ya nanata ƙudurin jihar na gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi mafi kyau a tarihin jihar ta Kano da ikon Allah ya yi addu’a neman tabbatar da zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply