INEC ta fara raba muhimman kayayyakin zaɓe a Yobe

0
365

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cewa ta fara raba muhimman kayan zaɓe a faɗin jihar Yobe.

Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Yobe Alhaji Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a harabar babban bankin Najeriya (CBN) reshen Damaturu.

“Muna saura kwanaki kaɗan da ranar zaɓen abin da muke yi a yanzu shi ne rabon wadannan kayayyaki masu muhimmanci ga jami’an zaɓe daban-daban.”

“Daga nan ne za a raba wadannan kayayyakin ga mazabu da rumfunan zaɓe a faɗin jihar.”

“Yayin da suke barin nan da kayan, daga nan za su je ofisoshinsu karkashin cikakken rakiyar jami’an tsaro da sojoji da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

KU KUMA KARANTA: Yadda Buhari ya ƙaddamar da ayyukan Gwamna Buni na jihar Yobe

“Wannan shi ne don tabbatar da cewa Kayayyakin sun isa lafiya don ci gaba da rarrabawa ga mazaɓun da rumfunan zaɓen da ke jihar ” in ji shi.

Kwamishinan hukumar zaɓen ya kuma ƙirayi duk waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a da su fito gaba ɗaya domin zaɓen mutanen da suke so a ranakun zaɓe.

Ibrahim Abdullahi ya ce: ” Ƙiran ya zama wajibi domin idan ba su fito ba, za su iya zama da shugabannin da ba sa so a bisa jagorancin su.”

Leave a Reply