Ina cikin waɗanda ƴan bindiga ke son kai wa hari — Dikko Radda

0
172

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya ce bayanan sirrin da ya samu sun nuna cewa yana daga cikin waɗanda ƴan bindiga ke son kai wa hari.

Ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a jihar a ranar Juma’a.

“Bayanan tsaro da muke samu wanda nima ina cikin wanda suke tunanin suna son su kai wa hari, duk muna samun waɗannan abubuwan amma ni wannan duk bai dame ni ba, ba zai sa mu yi ƙasa a gwiwa ba ga abin da muke yi ba Insha Allahu,” in ji gwamnan na Katsina.

Gwamna Radda ya bayyana cewa ƴan bingida na gayyato abokansu daga wasu jihohi domin garkuwa da mutane duk a yunƙurinsu na kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnatin na tabbatar da tsaro.

Gwamna Radda ya koka kan yadda kayan abinci ke ƙara tsada a ƙasar inda ya ce idan ba a bi a hankali ba yunwa za ta shiga cikin al’umma ta jawo tashin hankali da rashin zaman lafiya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sanye da hijabi sun afka wa ofishin ‘yan sanda a Katsina

Ya bayar da misali da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka soma a Jihar Neja da Jihar Kano sai dai ya ce akwai buƙatar duk da ba ta zo Katsina ba su ɗauki mataki domin magance ta.

Gwamnan ya ce daga cikin abubuwan da ke jawo wannan matsalar ta tsadar abinci akwai batun masu fitar da abincin da aka noma zuwa ƙasashen Nijar da Mali da Libiya da sauran ƙasashen maƙwabta sakamakon kuɗin ƙasashen sun fi na Najeriya daraja, wanda hakan yake sakawa su shiga Najeriya da kuɗi ƙalilan domin sayen abincin.

Haka kuma ya ce daga cikin masu taimaka wa wannan matsalar akwai jama’ar da ke fito da kuɗi daga gidajensu domin su sayi abinci idan ya yi tsada su sayar.

Leave a Reply