Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta kama shugaban ƙaramar hukuma bisa zargin badaƙalar sayar da filaye

0
19
Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta kama shugaban ƙaramar hukuma bisa zargin badaƙalar sayar da filaye

Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta kama shugaban ƙaramar hukuma bisa zargin badaƙalar sayar da filaye

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano ta kama Alhaji Abdullahi Mohammed, Shugaban Karamar Hukumar Kiru, bisa zargin sayar da filaye da darajarsu ta haura Naira miliyan dari (N100m) da aka tanadar domin gina filin wasa na Kafin Maiyaki Mini Stadium.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Kabir Kabir, ya tabbatar da kama wanda ake zargin.

Kabir ya ce binciken da suka gudanar ya gano cewa kudin an tura su ne kai tsaye zuwa cikin asusun ajiyar Abdullahi Mohammed.

KU KUMA KARANTA:Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wasu jami’an gwamnatin jihar kan zargin ɓatan naira miliyan 105

Ya ce a cewar binciken da suka yi, wani kamfani mai suna Mahasum ne ya sayi wadannan filaye da aka ware domin gina filin wasa.

A cewar Kabir, daga ranar 1 ga Nuwamba, 2024 lokacin da Mohammed ya hau mulki zuwa ranar 27 ga Fabrairu, an samu shigar kudi har Naira miliyan 240 a cikin asusun sa, wanda tuni aka kwato su.

Kabir ya kara da cewa Mohammed na ba da hadin kai a yayin da bincike ke ci gaba, domin gano gaskiyar lamari da kuma gurfanar da duk masu hannu a wannan badakala gaban shari’a.

“Hukumar na kokarin kawar da cin hanci da rashawa tare da tabbatar da gaskiya da adalci, inda ake ci gaba da tsare wanda ake zargi yayin da bincike ke gudana,” in ji shi.

Leave a Reply