Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wasu jami’an gwamnatin jihar kan zargin ɓatan naira miliyan 105

0
174
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wasu jami'an gwamnatin jihar kan zargin ɓatan naira miliyan 105

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wasu jami’an gwamnatin jihar kan zargin ɓatan naira miliyan 105

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta Kano ƙarƙashin jagorancin shugabanta Barr Muhuyi Magaji Rimin Gado, ta kama wasu jami’an ƙaramar hukumar nasarawa haɗi da babban maitamaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano Hon Mustapha Mai Fada bisa zargin wawure kuɗi kimanin Naira Miliyan Ɗari Da Biyar 105.

Wadanda aka kama sun hada da Daraktan Kula da Ma’aikata, da Ma’ajin Kudi na Karamar Hukumar Nasarawa.

KU KUMA KARANTA:Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar kafa hukumar tsaro ta jiha

Wata majiya ta bankado cewar an umarci ma’aikatan da su baiwa Mustapha Maifada Naira dubu dari da biyar domin gabatar da wani shiri, a maimakon haka sai aka tura masa Naira Miliyan ‘Dari Da Biyar wanda suka bayyana hakan a matsayin kuskure.

Lamarin ya faru tun a watan Nuwamba na Shekarar data gabata ta 2024.

Rahotanni sun bayanna yadda Hon Mustapha Maifada ya fara kashe kudin da aka tura masa inda aka ce ya sayi kadarori da motar hawa.

Hukumar Anti corruption karkashin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado na ci gaba da tsare su don fadada binciken.

Leave a Reply