Hukumar tace fina-finai ta ba da horo ga mata 50 don su zama daraktoci a Kannywood

0
6
Hukumar tace fina-finai ta ba da horo ga mata 50 don su zama daraktoci a Kannywood

Hukumar tace fina-finai ta ba da horo ga mata 50 don su zama daraktoci a Kannywood

Daga Jamilu Lawan Yakasai

A ƙoƙarinta na kawo ci gaba a harkokin shirya fina-finai a jihar Kano dama Nijeriya baki ɗaya, Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Alh. Abba El-mustapha ta bada horo na musamman ga mata har guda 50 kan dabarun yadda ake aikin daukar hoto tare da yadda ake bada umarni a yayin shirya fina-finai wato (Directing).

Da yake jawabi a yayin kaddamar da fara bada horon na musamman ga mata guda 50, Shugaban Hukumar Alh. Abba El-mustapha ya sanarda cewa wannan horon shine irinsa na farko a tarihin Masana’antar kannywood wanda aka zabi zankar mata domin koya musu wani bangarene na musamman daga cikin aikin shirya fina-finai sabanin yadda akasansu abaya da suke fito a iya bangaren shirye shirye na zahiri wato (Acting)

A jawabinsa yayin taron, kwamishinan yada labarai na Jahar Kano kwamarad Ibrahim Abdullahi Waiya ya taya wanda suka sami kansu a cikin tsarin bada horon murna tare da Jan hankalinsu da suyi kokarin fahimtar abinda za’a koya musu domin cimma nasarar da aka saka a gaba.

KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta dakatar da wani fim, ta gayyaci daraktan fim ɗin ofishinta

Kwamarad waiya ya kara yin kira ga mahalarta taron da suyi amfani da koyarwar addinin musulunci a dukkanin aiyukansu tare da girmama al’adar malam Bahaushe.

Itama da take jawabi a madadin wanda suka sami nasarar shiga cikin tsarin bada horon na musamman ga mata 50 yan Masana’antar kannywood Haj. Rashida maisa’a wacce Shugabace ga jarumai mata na kannywood godewa Abba El-mustapha tayi dangane da yadda yake gudanar da aiyukansa batare da nuna bangaranci ko banbancin ra’ayin siyasa ba inda tayi kira ga yan Masana’antar ta kannywood dasu cigaba da bawa Hukumar hadin Kai a Koda yaushe.

Wannan de wani bangarene daga cikin kudire-kudiren wannan Hukuma na samawa maza da mata matasa wata muhimmiyar hanya dazasu Kara dogara da kansu a Masana’antar tare da kawo tsafta ta yadda matan zasu rinka taka wata muhimmiyar rawa a bangaren daya shafesu cikin Masana’antar ta kannywood.

Leave a Reply