Connect with us

Labarai

Hukumar alhazai ta ƙasa ta tsawaita wa’adin rufe karɓar kuɗin aikin Hajji na 2024

Published

on

Hukumar Alhazai ta, Ƙasa, NAHCON, ta sanar da tsawaita wa’adin rufe karɓar kuɗaɗen aikin Hajjin bana.

Wata sanarwa da mataimakiyar daraktan sashin hulɗa da jama’a, Fatima Sanda Usara ta fitar a jiya talata, NAHCON, ta ɗage wa’adin zuwa 31 ga watan Janairu.

Ta ce ƙarin wa’adin ya biyo bayan koke-koken da malaman addini da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, gwamnonin Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki kan a tsawaita wa’adin.

A cewar Usara, duba da kiraye-kirayen da dumbin al’umma su ka yi kan tsawaita wa’adin ya nuna buƙatar samar da dama ga maniyyatan da su ke buƙatar zuwa aikin Hajji.

“Don haka NAHCON na da yakinin cewa kafin cikar wa’adin, tare da tallafawa daga takwarorinta, hukumar za ta iya tabbatar da ainihin farashin aikin Hajjin 2024.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta ba maniyyata aikin hajjin baɗi mako uku su fara biyan kuɗaɗensu

“Don haka ƙarin wa’adin ya ba da dama ga sabbin masu rajista don yin hakan kuma a ƙarshen watan Janairu, waɗanda ke buƙatar cika kuɗaɗen su ma za su iya yin hakan.

“Hukumar NAHCON na amfani da wannan dama wajen tunatar da maniyyata da sauran masu ruwa da tsaki cewa ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanya ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar rufe sanya hannu kan duk wasu kwangiloli, wanda ke nuni da kawo ƙarshen biyan kuɗaɗen da ake biya a asusun IBAN.

“Da wannan tsawaita wa’adin, ya rage wata guda kenan kafin NAHCON ta kammala biyan dukkan kuɗaɗen da suka ajiye a asusunta na IBAN na aikin Hajjin 2024.

“Wannan karin wa’adin, duk da cewa ya wuce jadawalin shirye-shiryen NAHCON, ya nuna yadda Shugaban Hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi ya jajirce wajen ganin an shawo kan matsalolin masu ruwa da tsaki.

“Ya kuma miƙa godiyarsa ga malaman addini, da hukumomin jiha, da gwamnoni bisa yadda suka bayar da shawarar a madadin mahajjatan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like