Hukumar Ƙidaya a Najeriya za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi miliyan biyu – Kwamishina

0
216

Ayodeji Ajayi, kwamishinan tarayya mai wakiltar Ekiti a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, (NPC), ya bayyana cewa za a ɗauki ma’aikatan wucin-gadi miliyan biyu da za su yi aikin ƙidaya.

Ajayi ya bayyana hakan a Ado Ekiti a ranar Alhamis a wani taron manema labarai don sanar da jama’a game da shirin ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi domin yin aikin.

Ajayi ya yi gargaɗin cewa duk wani ma’aikaci da aka ɗauka aka same shi da aikata rashin gaskiya kafin, lokacin da kuma bayan aikin to za a hukunta shi tare da wanda ya tsaya masa.

Domin tabbatar da ɗaukar mata da yawa a aikin, hukumar NPC ta bayyana cewa a jihar Ekiti za ta ɗauki mafi ƙarancin kashi 40 cikin 100 na mata a matsayin ma’aikatan wucin gadi domin gudanar da aiki.

Mista Ajayi, wanda tsohon shugaban ma’aikatan jihar Ekiti ne, ya ce: “Hukumar za ta ɗauki ma’aikatan wucin gadi a har mutane miliyan biyu a faɗin ƙasar nan domin gudanar da wannan shirin horarwa, wannan ya haɗa da ma’aikatan NPC da ma’aikatan wucin gadi da za a horas da su da sauran ƙwararru.

“Kuma duk wani matashi mai neman aikin yi, wanda ya shiga aikin kuma ya yi aiki mai kyau, hukumar za ta ba shi satifiket domin inganta aikinsa.”

Ya bayyana cewa, hukumar na yiwa galibin ma’aikata a ma’aikatan jiha da tarayya, da kuma ‘yan Najeriya masu sha’awar aiki, tare da tabbatar da gaskiya a matsayin ma’aikata, inda ya buƙaci masu sha’awar su nuna sha’awar shiga aikin ta adireshin yanar-gizo: censusadhocrecruitment.nationalpopulation.gov.ng.

Leave a Reply