Hisbah a Kano ta rufe wasu shagunan da ake caca
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar dake hani da mummuna da umarni da kyakkyawa Hisbah tayi aikin data saba a cikin watan Ramadan.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Sheikh Mujahedeen Aminuddeen ne ya bayyana cewar hukumar ta rufe wasu shaguna da ake gudanar da caca a ciki cikin wata mai alfarma na Ramadan.
KU KUMA KARANTA:Hukumar Hisbah a Kano ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu aikin banza
Hukumar tayi dirar mikiya a karamar hukumar minjibir dake Jihar Kano, inda suke kulle shagunan tare da kwashe kayan da ake gudanar da cacan duka dai karkashin jagorancin Kwamandan yankin.
Inda a karshe ya ja hankulan matasa da suji tsohon Allah, su mayar da hankulan su akan ibada.