Hezbollah ta kai hari da makamai masu linzami a Tel Aviv
Hezbollah ta sanar da cewa ta harba makamai masu linzami zuwa hedkwatar Hukumar Leƙen Asiri ta Mossad da ke kusa da Tel Aviv, tana mai cewar a nan ne aka kitsa harin baya-bayan nan da aka kai ƙungiyar ta Lebanon da ke ɗaukar makamai.
“Ƙungiyar Gwagwarmaya ta Musulunci ta ƙaddamar da amfani da makami mai linzami mai suna ‘Qader da misalin ƙarfe 6:30 a ranar Laraba, 25 ga Satumban 2024, inda ta nufi hedkwatar Mossad da ke wajen birnin Tel Aviv,” in ji Hezbollah a wata sanarwa da ta fitar.
“Wannan hedkwata ce ke da alhakin kisan gilla ga shugabanni da kuma fashewar na’urorin sadarwa,” in ji sanarwar, tana mai nuni ga kisan kwamandojinta a makon da ya gabata.
Ta kuma cewa an kai harin don nuna goyon baya ga jama’ar Gaza da “bayar da kariya ga Lebanon da jama’arta”.
A karon farko
Rundunar sojin Isra’ila ta ce “A karon farko” makami mai linzami da Hezbollah ta harba ya isa Tel Aviv, kuma garkuwar makamai masu linzami ta Isra’ila ta tare shi.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Hezbollah ta kai hari sansanonin soji da dama a Israila
“Wannan ne karo na farko da makami mai linzami na Hezbollah ya isa zuwa Tel Aviv. Rundunar Sojin Isra’ila ta tare makamin,” kakakin sojin ya faɗa wa AFP.
Hezbollah da Isra’ila da sun daɗe suna gaba da juna, a kowace rana na dab da fara kaiwa juna hari a kan iyaka tun bayan da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa Hamas ta kai wa Isra’ila hari a ranr 7 ga Oktoba.
Harin na Hamas ya janyo yaƙi a Gaza da ya shigar da Hezbollah da sauran ƙungiyoyin da Iran ke goya wa baya da ke Gabas ta Tsakiya.
Isra’ila ta ɗauke hankalinta daga Gaza zuwa Lebanon a ‘yan kwanakin nan.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla mutane 558 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a ranar Litinin – wanda shi ne rasa rayuka mafi yawa da aka samu sakamakon rikici a kasar tun bayan yaƙin basasar 1975 zuwa 1990.