Hedikwatar tsaron Najeriya ta ayyana neman mutane 97 ruwa a jallo

0
113

Hedikwatar tsaron Najeriya dake Abuja ta ayyana neman ɗaya daga cikin shugabannin haramtacciyar ƙungiyar ‘yan awaren Biafra, Simon Ekpa, ruwa a jallo.
An wallafa sunan Simon Ekpa a jerin sunayen mutanen da hukumomin sojan Najeriya ke nema tare da wasu mutum 96 suka fito daga sassan ƙasar daban-daban.

A jikin wani kwali me ɗauke da hotunan mutanen da ake tuhuma, hedikwatar tsaron tace ta ayyana sunayen mutane 97 da take nema ruwa a jallo saboda laifuffukan ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da barazanar ɓallewa daga najeriya.

Mafi shura a cikin mutanen da ake nema shi ne simon ekpa wanda ke iko da wani tsagi na haramtacciyar ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar biafara ta Ipob wanda kuma aka ɗorawa alhakin ayyana dokar nan ta zaman gida tilas a duk litinin a yankin kudu maso gabashin najeriya.

Daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar da sunaye da hotunan mutanen da aka ayyana nemansu.

Mutanen da ake neman da sun haɗa da; kwamandojin ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da masu tada ƙayar baya sun fito ne daga shiyoyin arewa maso gabas da arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da kuma kudu maso gabashin Najeriya.

A jikin kwalin dake ɗauke da hotuna da sunayen mutane 97 da ake neman a ba da bayanin shiyoyin da suka fito.

Bayanin ya bayyana cewar mutane 43 daga cikin sunayen da ake neman sun fito ne daga shiyar arewa maso yamma dake fama da matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun haɗa da jagororinsu irinsu Alhaji Shingi da Malindi Yakubu da Boka da Dogo Gide da Halilu Sububu da Ado Aliero da Bello Turji da Dan Bokkolo da Labi Yadi da Nagala da Sa’idu Idris da Kachalla Rugga da Sani Gurgu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya na neman wasu ma’aikatan CBN ruwa a jallo kan zargin satar dala miliyan shida

A shiyar arewa maso gabas kuwa kwamandojin ‘yan ta’addar da aka ayyana nemansu ruwa a jallo sun haɗa da; Abu Zaida da Modu Sullum da Baba Data da Ahmad da Sani Teacher da Baa Sadiq da Abdul Saad da Kaka Abi da Muhammad Khalifa da Umar Tella da Abu Mujahid da Malam Muhammad da Malam Dahiru Baga da Uzaiya da kuma Ali Ngule.

A shiyoyin arewa ta tsakiya da kudu maso gabashin Najeriya kuma an ayyana neman ‘yan bindiga da masu tada ƙayar baya da gaggan masu laifi 21 ruwa a jallo.

Mutanen sun haɗa da jagoran wani tsagi na ƙungiyar ‘yan awaren Biafra, Simon Ekpa da Chika Edoziem da Egede da Zuma da Thankgod Gentle da Flavor da Mathew da David Ndubuisi da High Chief Williams Agbor da Ebuka Nwaka da kuma Friday Ojimka.

Sauran ‘yan ta’addar da suka fito daga shiyyar kudu maso gabashin Najeriya sun haɗa da; Obeimisi Chukwudi da aka fi Sani da Dan Chuk da David Ezekwem Chidiebube da kuma Amobi Chinonso Okafor da aka fi Sani da Temple.

Leave a Reply