Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4

0
52
Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4

Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4

Aƙalla mutum huɗu ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hatsarin ya rutsa da wata mota ɗauke da fasinjoji 18 wadda ta taso daga Ado-Awaye a Jihar Oyo zuwa Abuja.

Wani jami’in Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), da ya ziyarci wajen da hatsarin ya faru, ya bayyana cewa barcin da direban ya yi ne sanadin hatsarin.

Ya ce hakan ne ya sanya motar dukan wata tirela da ke tafiya a gabanta.

Hatsarin ya sa motar ta shiga ƙarƙashin tirelar, lamarin da ya yi matuƙar muni.

“Direban tirelar bai ankara ba sai da mutane suka fara kururuwa suna cewa ya tsaya,” in ji jami’in FRSC ɗin da ya nemi a sakaya sunansa.

“Lokacin da tirelar ta tsaya, mutum huɗu sun mutu nan take.”

KU KUMA KARANTA: Wani jirgi da NNPCL ya ɗauka ya yi hatsari a Fatakwal

Direban motar da wasu fasinjoji ne suka ji rauni, amma tuni aka garzaya da su asibiti domin ba su kulawa.

Hatsarin ya ƙara nuna muhimmancin samun isasshen hutu a wajen direbobi musamman masu yin doguwar tafiya.

Hukumomi sun yi kira ga masu motocin haya da su tabbatar da cewar direbobi suna samun hutu don kaucewa irin wannan mummunan hatsarin.

Leave a Reply