Harin Boko Haram ya kashe sojojin ƙasar Chadi sama da 40

0
29
Harin Boko Haram ya kashe sojojin ƙasar Chadi sama da 40

Harin Boko Haram ya kashe sojojin ƙasar Chadi sama da 40

Rahotanni daga ƙasar Chadi na cewa sojojin ƙasar sama da 40 suka rasu sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kai wani sansaninsu.

Wannan na cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar a ranar Lahadi.

Ta ce mayaƙan Boko Haram sun kai harin ne sansanin soji da ke tsibirin Barkaram a yankin tafkin Chadi da ke Kudu Maso Yammacin ƙasar, wanda ke da iyaka da Najeriya.

Rahotanni sun ce da misalin karfe 10 na daren Lahadi mayaƙan suka ƙaddamar da farmakin, inda suka ci ƙarfin sama da sojoji 200 da ke wannan sansanin.

KU KUMA KARANTA: Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram sun koma ruwa

Sanarwar ta tabbatar da mutuwar sojoji aƙalla 40, yayin da majiyoyin yankin suka ce adadin sojojin da suka mutu sun haura 60, tare da jikkata wasu da dama.

Majiyoyin sun ce, maharan sun mamaye sansanin har zuwa wayewar garin Litinin, inda suka yi awon gaba da makamai da alburusai masu tarin yawa, bayan sun kone sansanin sojin.

Shugaban ƙasar, Janar Mahamat Idriss Deby, ya kai ziyara sansanin da safiyar ranar Litinin, inda ya kaddamar da rundunar Haskanite da za ta yi farautar maharan.

Leave a Reply