Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa da ta Islamic Jihad sun bayar da sharuɗɗa huɗu idan har ana so a samu nasara a yarjejeniyar tsagaita wutar da ake shirin yi da Isra’ila.
Daga cikin abinda suke nema har da barin mutanen da suka rasa muhallansu komawa gidajensu da ke Gaza.
Shugaban ɓangaren siyasa na Hamas Ismail Haniyeh da kuma wata tawaga ta ƙarƙashin jagorancin sakataren Islamic Jihad Ziyad al-Nakhalah sun haɗu a Tehran babban birnin Iran.
A wata sanarwa da Hamas ɗin ta fitar, ta ce domin tabbatar da wannan yarjejeniya ta yi nasara, dole ne a dakatar da hare-haren da ake kaiwa a Gaza, da janye dakarun da ke ƙawanya, da komawar waɗanda suka rasa muhallansu gidajensu da kuma barin kayan agaji shiga.